
Hukumar lafiya matakin farko a Najeriya ta ce za a sake jaddada rigakafin allurar Korona ga ƴan ƙasar waɗanda aka musu a karon farko.
Shugaban hukumar Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka ranar Juma’a a wani matakin hadin gwiwa da su ka ɗauka da ma’aikatar lafiya.

Ya ce za a sake yi wa mutanen da aka yi wa rigakafin sau biyu da kuma wadanda aka yiw a rigakafin sau ɗaya.

Sannan ya jaddada sharaɗiin yin allurar wanda ya ce sai an tabbatar mutum ya kai shekaru 18 a duniya, kuma waɗanda aka musu rigakafin Astra Zeneca da dangoginta sau biyu sai sunn kai watanni shida za a sake musu ta uku.
Su kuwa mutanen da aka yi wa rigakafin Jonson sau ɗaya za a sake musu a karo na biyu bayan watanni biyu da yi musu ta farko.
Shugaban ya ce za a fara allurar ne daga ranar 10 ga wtaan Disamban d amu ke ciki.
Wannan wani mataki ne da su ka sake ɗauka tun bayan ɓullar sabon nau’in cutar Korona na Omincron.