Rahotanni daga jihar Kaduna na nuni da cewar mutane 60 da aka sace a wata coci a jihar sun shaki iskar yanci.

Bayan shafe fiye da wata guda a hannun ƴan bindigan, daga bisani an saki mutane 60 da aka sace a cikin cocin.
Ƴan bindiga sun sace masu bautar ne yayin d asu ke tsaka da gudanar da ibada a cocin E,mmanuel Baptist da ke Kakau Daji a jihar Kaduna.

Shugaban ƙungiyar kiritoci ta CAN a Kaduna Rabaran Jiseph Hayab ne ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust a yau Asabar.

Sai dai bai yi ƙarin bayani ko an biya kuɗin fansa kafins akin mutanen na su ba.
Baya ga mutane 60 da aka saki akwai wasu mutane tara da ƴan bindigan su ka saki duka a yammacin ranar Juma’a.
Tuni mutanen da aka saki su ke kan kulawar jami’an tsaro kafin miƙa su ga iyalan su.
Jihar Kaduna ta yi ƙaurin suna wajen ayyukan masu garkuwa da mutane waɗanda a wasu lokutan ke halaka wasu.