Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

An tsinci gawarwakin wasu yara takwas a cikin wata mota da aka ajiye a kan titin Adelayo Jah-Micheal a Badagry ta jihar Legas.

Al’amarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Adekunle Ajisebutu ne ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi.

Ya ce “Yaran takwas an ce sun kulle kansu ne cikin wata motar da aka yasar a lokacin da suke wasa”.

“An gano gawarwakin su kuma an ajiye su a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry domin a tantance ainihin musabbabin mutuwarsu”.

Kakakin rundunar yan sandan ya kuma ce kwamishinan yan sanda a Legas Hakeem Odumosu ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan al’amuran da suka shafi mutuwarsu.

Odumosu ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin a shafa.

A na zargin hudu daga ciki yaran yan gida daya ne da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: