Rundunar ƴan sandan jihar Osun ta tabbatar da kama wani jami’in ta guda bisa zargin harbe wani direban mota a jihar.

Ana zargin ɗan sandan da kashe wani mai suna Malama Kabiru mai shekaru 33 a duniya wanda hakan ya yi silar mutuwar sa.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar SP Yemisi Opalola ce ta sanar da kama jami’in ɗan sanda Sajan Moses Samuel bayan an zarge shi da nuna rashin ƙwarewa a bakin aiki.

Yemisi ta ƙara da cewar al’amarin ya faru ne a ranar Juma’a a Osogbo ta jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya nuna takaici a bisa rashin ɗa’ar da jami’in nasu ya yi da kuma nuna rashin ƙwarewa a bakin aiki.

Sannan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan direban da aka kashe.

Sanarwar da kakakin ta fityar ranar Lahadi ta ce an fara bincke a kan wanda ake zargi kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kan sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: