Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a ranar Litinin ya haramtawa kungiyar kwararrun mafarauta ta Najeriya gudanar da ayyukanta a fadin kananan hukumomin jihar 21 saboda al’amuran tsaro.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou.

Gwamnan ya kara da cewa ayyukan mafarauta na iya haifar da koma baya a al’amuran tsaron jihar.

Don haka ya kamata su daina yin duk wani aiki da sunan samar da tsaro ga jama’a.
Fintiri ya ce “Ayyukan kungiyar a kananan hukumomi biyar sun zama abin damuwa da rashin tsaro, maimakon samar da tsaro wanda ake tsammanin ganin haka daga gare su”.
A halin yanzu gwamnatin jihar ta dakatar da dukmanin ayyukan mafarauta a faɗin jihar ba tare da saka ranar koma wa ba.