Hukumar alfiya ta duniya NCDC ta ce an same samun mutane uku ɗauke da sabon nau’in cutar Korona na Omicron.

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yau Talata.
Hukumar ta ce mutane ukun da ke ɗauke da cutar sun ziyarci ƙarsar Afrika ta Kudu.

Kafin samun karin mutanen an samu wasu mutane uku a baya tun a farkon watan da mu ke ciki.

A sakamakon samun ɓullar Omicron a Najeriya ƙasashen Canada da Burtaniya su ka haramta wa ƴan Najeriya shiga ƙasashen su.