Akalla mutane 15 ne su ka rasa rayukansu yayin da wasu da yawa su ka samu munanan rauni a wani hari da yan bindiga su ka kai jihar Neja.

An kai harin wani masallaci da ke ƙauyen Ba’are a ƙaramar hukumar Mashegu ta jihar.

An kashe mutanen su na tsaka da salar asuba a yau Alhamis.

Kwamishinan ƴan sansan jihar ya tabbatar da kai harin.

Ya ce an tafi da mutanen da su ka samu rauni zuwa asibitin Kontagora domin duba lafiyasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: