Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban hafsan sojin kasan Najeriya a gaban kotu bisa zargin karkatar da kuɗin makamai.
An gurfanar da Laftanar Janar Kenneth Minimah (mai ritaya) da wasu manyan sojoji bisa zargin karkatar da kudaden siyan makamai nairabiliyan 13.

Hukumar EFCC ta shigar da kara a gaban babbar kotun tarayyar da ke Abuja bayan gudanar da bincike a kan manyan sojojin.

A na zargin tsohon babban harsan sojin da karkatar da kuɗaɗen makamai da su ka yi bayan karɓar rahoto daga wani kwamiti da ya gudanar da bincke a shekarar 2016.
Ana zargin babban hafsan sojin Najeriya da sauran manyan darantocin gudanarwar kuɗi a rudunar sojin sama da ƙasa da na ruwa da wawure kuɗaɗen siyan makamai.