Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Legas da ke kudancin ƙasa don buɗe ayyuka.

An tsaurara matakan tsaro tare da sauya wa mutane wasu hanyoyin da za su bi a maimakon wanda su ke bi don ziyarar shugaba.
A na sa ran shugaban zai kaddamar da wasu jiragen yaƙi na ruwa da kuma wasu ayyuka a birnin na Legas.

Haka kuma shugaban zai halarvi ƙaddamarda wani littafi wanda Bisi Akande ya rubuta.

Hakan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 48 da kisan matafiya wanda ƴan bindiga su ka kone su da ransu a jihar Sokoto.
Shugaban yaaike da saƙon ta’aziyya ga iyalan mutanen da aka kashe.