Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sabon nau’in annobar Korona yatsallaka zuwa ƙasashe 57 na fɗin duniya.

Babban darakta a hukumar Tedros Ghebereyesus ne ya sanar da haka yayin gana wa sa manema labarai.
Ya ce yaɗuwar da cutar ke yi ta sa sun gaza gano adadin mutanen da ke ɗauke da ita a yanzu.

Daraktan ya bayyana yaɗuwar cutar cikin sauri fiye da sauran nau’in cutukan baya.

Sannan ya shawarci al’umma da su dinga bin dokokin kariya daga cutar don han yaɗuwarta.
Kuma ya hori jama’a da su yi allurar riga-kafin cuta don tseratar da rayuwarsu.