A wani sakon ta’aziyya da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar ya ce bai ji daɗin yadda lamarin ya kasance ba.

Ya ce wannan al’amari na bukatar gudumawar dukkanin al’umma don magance matsalar.

Shugaban Najeriya Buhari ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da aiki tukuru don ganin an magance matsalar tsaaro da ta addabi kasar.

Ƴan bindiga sun kone matafiya da ransu a cikin mota a jihar Sokoto.

An tare matafiyan a kan hanyar su ta tafiya.

Tuni aka yi jana’izar mutanen da su ka mutu a sanadin mummunan harin.

A na zargin mutanen da aka kashe sun kai su 23 kuma daga ciki har da jariri sabuwar haaihuwa.

Matsalar tsaro nna ci gaba da yaɗuwa ƴan bindiga na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare dun da bayanan da gwamnati ke cewa ta na samun galaba a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: