Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta sake barazanar shiga yajin aiki a ƙasar a ranar Juma’a.

Hakan na zuwa ne bayan wani zama da ƙungiyar ta yi tun lokacin da ta sanar da yunkurin ɗaukar wai mataki cikin sa’o’i 48.
Ƙungiyar ta gudanar da taron bayan gargaɗin da ta yi wa gwamnatin ƙasar don ganin ta biya musu bukatun su.

Ƙungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin ne bayan da bangaren gwamnatin ya ƙi mutunta yarjejeniyar da su ka yi bayan zaman sulhu da aka yi a baya.

Ƙiungiyar malaman jami’a a Najeriya na neman wasu haƙƙoƙin yaƴan kungiyar na kudaɗe da su k a maƙale daga gwamnatin ƙasar.
Sannan ƙungiyar ta musanta raɗe-raɗin da ake na cika wasu alƙawura da gwamnatin ta yi a shekarar 2020.