Rahotanni daga jihar Borno ta tabbatar da cewar wasu da ake kyauta zaton mayaƙan Boko Haram ne sun sace wasu matafiya a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

An sace matafiyan ne yayin da su ke gab da shiga Maiduguri bayan sun taso daga Damaturu ta jihar Yobe.

Matafiyan na koƙarin shiga garin a safiyar yau Asabar sai dai mayakan sun tafi da su cikin daji.

Karo na hudu ke nan a na sace matafiya a ƴan kwanakin nan.

A baya an sace wasu ma’aikatan gwamnati da kuma wasu matafiya da ake zaton sun kai su 15.

Mutanen da aka sace a safiyar yau ba a kai ga gano adadin su ba.

Wani shugaba a yankin ya tabatar da faruwar lamarin, wanda ya ce an tare matafiyan ne da misalin ƙarfe 08:30 na safiyar yau.

Ya kara da cewa an sace matafiyan a tsakanin Mainok da Benisheiek da ke ƙaramar hukumar Kaga a jihar Borno.

Leave a Reply

%d bloggers like this: