Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da kai harin da aka yi a yammacin Lahadi.

Aƙalla mutane goma ne su ka mutu a sakamakon harin ƴan bindiga a jihar Filato.
Ƴan bindiga sun kai harin ne jim kadan bayan kammala cin wata kasuwar mako-mako a jihar.

Rahotanni na nuni da cewar an kai harin a yammacin Lahadi kuma akwai wasu da dama da su ka samu munanan raunuka a sanadiyyar harin.

Wani mazaunin garin Pinau a ƙaramar hukumar Wase ta jihar ya tabbatar da hakan kuma ya ce su na zargin ƴan bindigan sun je garin ne daga jihar Zamfara.
Daga ɓangaren ƴan sandan jihar ma sun tabbatar da faruwar al’amarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar ASP Gabriel Ubah ya ce sun sami labarin kai harin sai dai bai yi wani ƙarin haske a dangane da abin da ya faru ba.
Wasu rahotanni na nuni da cewar ƴan bindigan da ke shan matsin lamba daga jami’an tsaro a jihar Zamfara na shiga wasu jihohin maƙofta don ƙaddamar da hare-hare.