Connect with us

Labarai

Abubuwan Da Masari Ya Ce Yayin Zuwansu Abuja Yau

Published

on

Daga Amina Tahir Muhammad Riskuwa

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce akwai bukatar dukkan jihohin da ke Arewa maso Yamma su hada kai don magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ya jagoranci tawagar dattawa jihar sa don ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Masari “Ina ganin abin da ya fi dacewa mu yi nasara wajen yakar wadannan ‘yan ta’adda shi ne mu duka jihohin mu, musamman Arewa maso Yamma.

“Amma idan wata jiha tana da manufa, wata kuma tana da wata manufa ta daban, to tabbas su (’yan bindiga) za su rika tafiya daga wannan jiha zuwa waccan. An yi sa’a, mun riga mun hada gwiwa da Jihohin da ke kan iyaka da mu, kamar Nasarawa da Neja, don kawo karshen matsalar.”

Dan gane da kisan da a kayi wa daya daga cikin kwamishinonin sa a baya-bayan nan Masari ya ce lamarin bashi da alaka da yan fashi ya na mai bayyana hakan a matsayin kisan gilla.

Gwamnan ya tabbatarwa da iyalan mamacin da ‘yan jihar cewa jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen bankado musabbabin kisan.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Sama Da Mutane 85 cikin 100 Na Amfana Da Tallafin Wutar Lantarki

Published

on

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan janye tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

 

Ministan ya ce sama da Naira tiriliyan 1 da za a samu sakamakon janye tallafin wutar lantarki, za a yi amfani da su wajen inganta samar wutar lantarki da ayyukan more rayuwa a ƙasar nan.

 

Jaridar The Nation ta ce Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a jiya lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin ‘Hannu da Yawa’ na Rediyo Najeriya da ke Kaduna.

 

Ministan ya ce wasu ƴan tsiraru masu hannu da shuni da kamfanoni ne kawai ke kwashe garaɓasar tallafin wutar lantarkin.

 

A cewarsa kaso 40% na tallafin wutar lantarkin yana amfanar kaso 15% da ke samun wutar lantarki ta sa’o’i 20 a kowace rana.

 

Idris ya jaddada cewa har yanzu kaso 85% cikin 100% na al’ummar da suke ƙarƙashin sauran rukunonin wutar lantarkin na samun tallafi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano Ya Nuna Bacin Rai Kan Sakin Yan Daba A Kano

Published

on

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka saki ‘yan daba da ke kulle a jihar.

Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kawo tsaiko a kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar dabanci a jihar.

Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati.

Ya bayyana yawan ‘yan dabar da aka kama domin yi musu hukunci amma abin takaici an sako su.

Har ila yau, gwamnan ya zargi jam’iyyun adawa da kokarin kubutar da ‘yan dabar domin biyan buƙatar kansu ta siyasa.

Continue Reading

Labarai

Jagororin APC A Ondo Sun Zargi Gwamnan Jihar Da Yin Makarkashiya A Zaben Fidda Gwani

Published

on

Wasu jagororin jam’iyyar APC a Jihar Ondo sun zargi gwamnan Jihar Lucky Ayedatiwa akan kulla makarkashiya akan zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Afrilu da muke ciki.

 

 

 

Jagororin jam’iyyar karkashin wata kungiya mai rajin tabbatar da shugaban nagari a Jihar sun ce gwamnan na kokari sauya zaben na fidda gwani.

 

 

 

Shugaban kungiyar Evangelist Tade Ojo ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikewa da shugaban kasa Bola Tinubu kan lamarin.

 

 

 

Shugaban ya ce gwamnan tare da magoya bayansa sun buga katuna da tambarin jam’iyyar su na rabawa mutanen da ba mambobin jam’iyyar ba.

 

 

 

Shugaban ya bukaci jam’iyyar APC ta kasa da shugaban kasa Tinubu da su dakatar da Ayedatiwa akan yunkurin tarwatsa zaben na fidda gwani.

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: