Akalla mutane 20 ne su ka rasa rayukan su a wasu hatsarin mota da su ka faru a jihar Bauchi.

Hatsarin farko ya faru a yammacin Lahadi yayin da wasu motoci biyu su ka yi karo a kan babbar hanyar Kano zuwa Jama’are.

Hatsari na biyu kuwa babbar mota ce da wata motar fasinja mai ɗauke da gurbin mutane 18 a ciki.

Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a jihar Bauchi Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kuma ya danganta afkuwar haɗɗuran da gudun wuce sa’a wanda hukumar ke bayyana cewar na haifar da rasa rayuka da ma dukiyoyi.

Ya ce an garzaya da gawarwakinmutanen babban asibitin Kiyawa kuma a nan ne likitoci su ka tabbatar mutanen sun rasu.

Ya ce hatsari na biyu ya faru ne a Duhuwar Kura ƙauyen da ke kan hanyar Azare zuwa garin Zaki.

A sanadin haɗɗuran akwai wasu da su ka jikkata kuma tuni su ke kan kulawar likitoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: