Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta tabbatar da kama wasu mutane shida da ake zargfi da kashe wasu masu ibada a Maza-Kuka, da ke ƙaramar hukumar Mashegu a jihar.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Wasiu Abiodun ne ya sanar da haka bayan kwamishinan tsaro a jihar ya tabbatar da kama wasu daga ciki.

Tun da farko kwamishinan tsaro a jihar Emmanuel Umar ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a wani taron manema labarai da ya yi a ranar Laraba a Minna babban birnin jihar.

Emmanuel Umar ya ce an kama wasu daga cikin maharan sai dai bai bayyana adadin mutanen da aka kama ba.

Yayin da yake amsa tambaya daga ƴan jarida, kakakin ƴan sandan jihar ya tabbatar da kama mutane shida wanda ya ce ana zargin su da hannu wajen kai harin.

Ana ci da bincike a kan mutanen da ake zargi kamar yadda kakakin ya bayyana.

A kwana nan dai da ƴan bindiga su ka kai hari wani masallaci a jihar tare da kashe masallata yayin da su ke tsaka da sallar asuba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: