Rahotanni daga jihar Nassarawa na tabbatar da cewa cutar Lassa ta hallaka wasu ƙwararrun likitoci a jihar.

Likitocin sun rasa rayukansu a asibitin Dalhat Arafat Special Hospital da ke Lafiya babban birnin jihar.

Mai magana da yawun asibitin Ruth Namo ta tabbatar da hakan ta ce likitan farko ya mutu a makon da ya gabata yayin da ɗaya likitan ya mutu a jiya Laraba.

A na zargin likitocin sun kamu da cutar ne yayin da su ke yi wa wata mata aikin gaggawa bayan an sameta da cutar.

Hukumar lafiya a ajihar tagargaɗi mutane da su kula da dukkanin abin da za su ci don gudun kamuwa da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: