Hukumomi a jihar Kaduna sun ce ƴan bindiga sun hallaka mutane tara a wasu hare-hare da su ka kai wurare daban-daban na cikin jihar.
Kwamishinan al’amuran tsaro a jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da haka ya ce an kashe mutanen ne a Zaria, Zangon Tataf da ƙaramar hukumar Chikun.
Ya ƙara da cewa an kashe mutane uku a harin da ƴan bindiga s8u ka kai garuruwan Udawa da Buruku.
Sai kuma mutum guda da aka kashe a yayin da su ka kai hari garuruwan Kadi da Yola waɗanda ke ƙaramar hukumar Chikun.
Sa’annan ƴan bindigan sun kai harin ƙauyen Sako da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf tare da kashe mutane biyu bayan nan kuma an gano gawarwakin mutane biyu a yankunan Kurfi da Magamiya.
A ƙauyen Saye da ke ƙaramar hukumar Zaria ma an kashe mutum guda a cewar sanarwar.
Kwasmishinan tsaron ya ce su na kan aiki tuƙuru da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Kaduna.
Sanarwar ta ce gwamnan jihar Malam Nasir El’rufa’i ya nuna takaici a kan lamarin tare da yin Alla-wadai da faruwar lamarin.