Gwamnatin jihar Nassarawa ta haramta amfani da gawayi da ma siyar da shi a fadin jihar baki ɗaya.

Babban sakatare a ma’aikatar muhalli a jihar Aliyu Agwai ne ya sanar da umarnin hakan yau Asabar a Lafia babban binrin jihar.

Ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne ganin yadda hakan ke gurɓata muhalli tare da taimaka wa wajen ɗumamar yanayi.

Ya ƙara da cewa sare bishiyoyi da ake yi a jihar tare da ƙone su domin samar da gawayi hakan babbar barazana ce a jihar.

Haka kuma dabbobi ma na rasa yadda za su yi a sanadin yawan sare bishiyoyin da ake yi.

Matakai ke nan da gwamnatin ta duba tare da ɗaukar matakin haramta siyar da gawayi da kuma ƙona itace don samar da gawayin.

Al’ummar Najeriya sun koma amfani da gawayi ka’in da na’in tun bayan da gas ya ci gaba da tashin gwauron zabi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: