Mutane na ta tofa albarkacin bakin su a kan shirin shirin da aka yi a kan auren WUFF .

An tattauna da malama Sadiya Sani a cikin shirin Sirrin Ma’aurata wadda ta yi jawabi a kan auren babba namiji da kuma mace mai ƙarancin shekarau.
Malamar ta zayyano wasu matsalolin da matan kan iya fuskanta yayin da tafiya ta yi tafiya acikin aure.

Ta ce auren da ake yi tsakanin mace ƙarama da namiji mai shekaru na da haɗari.

Ta bayar da misalin yadda wasu kan kasa biya wa matan buƙata ko da su na so amma saboda girma da ya kama su sai ya kasa.
A lokacin da mace ta kai shekaru 30 a duniya jikinta na buƙatar wannan saƙon (Ɗa namiji) sai dai ba su cika samun gamsuwa daga mazajen su ba musamman waɗanda su ke masu shekarun da su ka haife ta ko ma su ka yi jika da ita.
Mutane na kalklon hakan a matsayin wata sarƙaƙƙiya da ya kamata a sake duba wa ganin cewar maza na ta tofa albarkacin bakin su a kai.
Wasu na daga cikin matan na kallon hakan a matsayin daidai yayin da wasu ke kallon hakan da wata manufa ta daban.