Gwamnatin jihar Neja ta bayar da umarnin rufe makarantu an firamare da sakandire da ma na gaba da sakandire a karamar hukumar Wushishi ta jihar.

Shugaban karamar hukumar Wushishi Danjuma Suleiman Nalango ne ya bayar da umarnin hakan bayan samun bayanai a kan shirin sace wasu dalibai a kusa da karamar hukumar.

Ya ce sun samu bayanin sirrin ne daga jami’an tsaro kuma gudun sace daliban ne ya sa za a rufe makarantun.

Akwai bayanai da ke nuni da cewar yan bindiga na yunkurin sace dalibai a makarantar kimiyya da wata makarantar mata ta Zungeru.

Jihar Neja na daga jihohin da yan bindiga su ka addaba tare da sace dalibai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: