Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da haramta duk wani nau’in biki a cikin harabar makarantun jihar ta.

Babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta jihar Dakta Yusif Saleh ne ya sanar da haka a yayin da yake gana wa da manema labarai a Kuduna.

Gwamnatin jihar ta ɗauki matakin haka ne domin kare kayayyakin makarantun daga yadda ake lalata su.

Ya ce a kowacce rana su na karɓar ƙorafi a kan yadda ake lalata kayayyaki a makarantu kuma hakan ke lashe kuɗaɗe masu yawa wajen gyara wa.

Ya ce za su tabbatar tsarin ya ɗore ta hanyar hada kai da ma’aikatar harkokin cikin gida a Kaduna domin tabbatar da dokar.

Sannan matakin da su ka ɗauka zai ƙara taimaka wa a bangaren tsaron da jihar ta ke fuskanta na hare-haren masu tayar da ƙayar baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: