Hukumar kula da gidajen gyaran hali a Najeriya za ta samar da wasu jami’ai na musamman wadanda za su dinga bai wa gidajen yari kulawa ta musamman domin kare gidajen daga hare-hare a Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar a Najeriya Francis Enobore ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce babban kwantirola a hukumar Halliru Nababa ne ya sanar da haka yayin da ya ke gana wa da shugaban hukumar shige da fice da kuma babban kwamandan hukumar kare fararen hula ta Civil Defence.

Shugaban ya ce taron da su ka yi ya kalli batun yadda za a samar da jami’ai na musamman ta hanyar shawarwarin abokan aikin su.

Ya ce za a samar da jami’an tsaron hadin gwiwar cikin gaggawa bisa umarnin da ma’aikatar harkokin cikin gida ta bayar.

Jami’an tsaron da za su yi hadin gwiwar akwai sojoji, ƴan sanda waɗanda tuni aka kai wasu da dama domin bayar da kariya ta musamman a kan gidajen yarin.

Wasu da ba a san ko su waye ba na kai hare-hare gidajen yari a Najeriya musamman kudancin ƙasar tare da kuɓutar da masu laifi a ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: