Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta ce an samu tashin gobara guda 706 maimakon 786 da aka samu a shekarar da ta gabata.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar SFS Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana haka a yayin ganawar sa da Matashiya TV yau Talata.
Ya ce sun sami nasarar kuɓutar da dukiyar da ta haura naira miliyan 614.

SFS Saminu ya ƙara da cewa a tsakanin watanni 11 na shekarar 2021 sun samu kiran gaggawa guda 743, yayin da su ka karɓi kiran ƙarya guda 171.

A sakamakon haɗɗura da gobara cikin watanni 11 an samu asarar dukiyar da ta kai naira miliyan ɗari da casa’in da takwas da dubu ɗari tara da saba’in da biyar da ɗari tara da talatin da ɗaya (198,975,931).
Haka zalika sun tabbatar da mutuwar mutane 132 yayin da su ka tseratar da rayukan mutane 1,139.
A ɓangare na haɗɗura kuwa sun karɓi rahoton haɗɗura guda 581 sai mutane 110 waɗanda su ka faɗa cikin ruwa sannan mutane 31 waɗanda su ka faɗa cikin rijiya.
SFS Saminu Abdullahi ya ja hankalin mutane da su dinga sa ido musamman a wannan lokaci na sanyi da ake yawan samun tashin gobara.
Hukumar ta alaƙanta yawan tashin gobara da sakaci wajen amfani da wutar lantarki da kuma amfani da gas ɗin girki sai kuma wuta mai amfani da harken rana.
Hukumar ta bayar da wasu lambobin da za a kira idan an samu buƙatar hakan a jihar Kano, lambobin su ne kamar haka 08107888878, 07051246833, 07026026400, 08098822631.