Fiye da shaguna 300 gobara ta laƙume a kasuwar Kara a jihar Sokoto.

Gobarar da har yanzu ba a kai ga gano dalilin  faruwarta ba ta fara ne da misalin ƙarfe 2:0am na dare.

Shugaban kasuar Alhaji Chika Sarkin Gishiri ya ce gobarar ta ƙone dukiya mai yawa a kasuwar.

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya jajana a bisa faruwar gobarar wadda ta ƙone shagune da dama.

A yanayin sanyi a kan samu yawan faruwar gobara da dama sai dai har yanzu hukumomi ba su bayar da cikakken bayani a kan sanadiyyar tashin gobarar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: