Matafiya da dama sun rasa hanyar wucewa a sakamakon tare babbar hanyar Funtua zuwa Gusau da wasu mutane su ka yi.

Mutanen sun tare hanyar ne domin nuna baƙin cikin su a kan hare-hare da ake kai musu.
Wani ya shaida cewar ƴan bindiga sun kai hari wasu yankunan a Faskari tare da kashe mutane sannansu ka sace mata biyar.

Ƴan bindiga sun kai harin en a ranar Litinin da misalin ƙarfe tara na dare.

Rahotanni na nuni da cewar ƴan bindigan sun kai hare-hare sau huɗu a ƙasa da kwanaki bakwai.