Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a Najeriya FRSC reshen jihar Kano ta sanar da cewar mutane 250 ne su ka rasa rayukansu a sakamakon haɗɗuran da su fa faru cikin shekarar 2021.

Kakakin hukumar SRC Abdullahi Aliyu Labaran ne ya sanar da haka yayin ganawar sa da Matashiya TV ranar Talata.
Ya ce an samu afkuwar haɗɗura sau 270 a shekarar 2021.

Abdullahi Labaran ya ce haɗɗura sun ragu la’akari da shekarar da ta gabata.

Ya ƙara da cewa binciken da su ka gudanar ya nuna musu cewar gudun wuce sa a da ɗaukar kayan da su ka zarce ƙa’ida ne ke haifar da mafi yawan haɗɗuran.
A dukkanin ƙarshen shekara a kan samu yawan tafiye-tafiye wanda hakan ke haifar da haɗɗura a wasu lokutan, kakakin ya ja hankalin masu tuƙa ababen hawa da su lura domin kare kan su da lafiyar su da ma rayuwarsu.