Daga Amina Tahir Muhammad

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, inda suka yi awon gaba da wasu mutane hudu.
Wani mazaunin garin Tella mai suna Suleiman Rabiu ya shaida cewa ‘yan bindigar kimanin 12 sun kewaye masallacin ne da misalin karfe 7:12 na dare inda suka yi awon gaba da wasu masallata da suke sallar Isha’i.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar bayan sun tarwatsa taron addu’o’in ne suka fitar da masallatan daga Masallacin da bindiga.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun sake sakin mutum daya sannan suka tafi da sauran inda ba a sani ba.
Daga cikin wadanda aka sace akwai Alhaji Yahaya da Aminu Dali da kuma Alhaji Hussaini wanda shi ne shugaban dillalan hatsi a yankin
Mazauna yankin Gassol na fuskantar hare-hare daga wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka kaura daga jihar Zamfara zuwa yankin bayan farmakin da sojoji suka kai musu.
A cikin makonni uku da suka gabata, an yi garkuwa da mutane sama da 25, galibi ‘yan kasuwa da manoma.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi cikakken bayani ba.