Daga Amina Tahir Muhammad

Hukumar tsaron fararen hula ta Najeriya (NSCDC) reshen babban birnin tarayya Abuja ta aike da jami’anta 3000 domin sa idanu a kan bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
Kwamandan hukumar a babban birnin tarayya Abuja, Dakta Peter Maigari, shi ya sanar da haka a yau Alhamis.

Ya bayyana cewa an yi hakan ne da nufin samar da tsaro da ake bukata ga muhimman kadarorin gwamnati da mazauna babban birnin tarayya Abuja da kewaye a wannan lokacin na Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Ya ci gaba da cewa wannan bai rasa nasaba da umarnin da babban Kwamandan Rundunar NSCDC ta kasa Dakta Ahmed Audi wanda ya bayar da umarnin tabbatar da tsaro da kuma hada kai da sauran hukumomin tsaro.
Sanarwar hakan na kunshe cikin wata sanarwar da aka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun Comfort Okomanyi, kakakin rundunar ta Abuja.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na ganin an kare kadarorin gwamnati daga barna a fadin babban birnin tarayya Abuja.
Kwamandan Maigari ya bayyana cewa zaman gidan yari na shekaru 21 ba tare da zabin tara ba yana jiran duk wanda aka kama da laifin lalata kadarorin gwamnati.
Ya karfafa wa mazauna babban birnin tarayya Abuja da su wanzar da zaman lafiya da bin doka oda a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.