Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci ƴan ƙasar su je a musu riga-kafin annobar Korona.

Shugaban ya yi wannan kira ne a cikin sƙon kirsimeti da ya aike wa ƴan ƙasar musmaman mabiya addinin kirista.
Ya ce ya kamata ƴan ƙasar su je a musu riga-kafin domin rage yaɗuware cutar.

Shugaban ya ce gwamnatin sa za ta tabatar ta cika alƙawuran da ta ɗauka tun lokacin yaƙin neman zaɓe.

Muhammadu Buhari ya ce ba za su yi watsi da alƙawuran da su ka ɗauka a har sai sun tabbatar sun cika su kafin wa’adin mulkin sa ya cika.