
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya ta taimaka wa gwamnoni domin shawo kan matsalar tsaro a jihohin da ake fuskantar rashin tsaro.
Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da ya je fadar shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a.

Gwamna Ganduje ya ce mafi yawan dazukan ƙasar na ɗauke da ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane, ƴan fashi da makami da sauran masu aikata muggan laifuka.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar samar da sansanin horas da sojoji a dazukan da ke iyakokin jihohin Kano, Plateau, Bauchi da Kaduna.
Gwamnan ya ce ya je ganin shugaba Buhari ne domin sanar da shi halin da ake ciki na tsaro a jihar Kano tare da ƙalubalen da ake fuskanta.
Ya ce mafi yawan dazukan ƙasar na ɗauke da masu aikata manyan laifuka kuma ita ce babbar matsalar da gwamnoni su ke fuskanta.
Kuma samar da sansanin horas da sojoji a sauran dazukan zai taimaka wajen rage masu laifi da samun mafaka a cikin dajin.
Ganduje ya yaba wa shugaba Buhari a kan ƙoƙarin da yake a ɓangaren tsaron ƙasar wanda ya ce duk da haka su na buƙatar taimakon gwamnatin sa domin ƙarfafa tsaro a sauran jihohi.
Gwamna Ganduje ya ziyarci shugaba Buhari ranar Juma’a kwana guda gabanin yau da ya ke cika shekaru 72 a duniya.