Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura FRSC reshen jihar Ogun ta sanar da mutuwar mutane 6 da kuma wasu mutane 12 da su ka samu rauni a wani hatsari da ya faru.

Kwamandan hukumar Ahmed Umar ne ya sanar da haka a Ota ta jihar Ogun.
Ya ce al’amarin ya faru ne a da misalin ƙarfe 3:20 na daren Juma’a wayewar yau Asabar.

Mutane 18 hatsarin ya rutsa da su kuma 12 daga ciki sun samu munanan rauni.

An ajiye gawarwakin mutanen da su ka mutu a asibitin Idera da ke Sangamu yayin da aka kai waɗanda su ka samu rauni asibitoci daban-daban domin ceto rauwarsu.
Haka kuma hukumar ta tseratar da wasu kuɗaɗe da su ka kai naira 127,900 a wajen da abin ya faru.
Sai dai hukumar ta zargi cewar gudun wuce sa a ne ya haifar da hatsarin wanda hakan yayi silar rasa sarrafa motar daga direban.
Kwamadan ya bukaci matuƙa ababen hawa da su dinga bin dokokin tuki domin kare rayuka da lafiya da ma dukiyoyin su.