Shehin malamin ya yin ƙarin haske a kan fatawar da ya bayar a kan halascin sauraron waƙa da kuma rerawa.

Malamin ya ce sauraron waƙa ko rerawa ya na da matuƙar amfani ga lafiya da rayuwar mutane.

A cikin wata tattauna wa da BBC su ka yi da malamin ya ce sauraron waƙa ya na ƙara wa garkuwar jiki lafiya da kuma saka kuzari da buda tunani da maganin zafin jiki.

Malamin ya sha suka a wajen wasu malamai a kan yadda ya bayyana a wani karatun sa da ya ce jin waƙa halak ne kuma wanda ba ya sauraron waƙa ya na cutar kan sa kuma ya jahilci kan sa.

Malamin ya ce manzon Allah S.A.W ya na jin waƙa kuma ya na saka wa a rera masa waƙa.

Sai dai malamin ya ce sauraron waƙa ba laifi ba ne matuƙarkalaman ciki ba su kasance na haram ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: