Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun dace wsu matan aure da ƴan mata su 33 tare da kashe wasu maza a wasu ƙauyuka da ke jihar Zamfara.

Maharan sun afka garuruwan ne a ranakun Asabar da Lahadi tare da kashe mazajen su sannan su ka wuce da matan aure da yan mata a ƙauyukan.

Ƴan bindigan sun shiga ƙauyukan Gebe, Tsakuwa, Gidan Ƙaura, Gana, Ƙura, Bayauri, Ketare Duma da wasu ƙauyuka duka  aƙaramar hukumar Gusau babban birnin jihar.

Baya ga mata 33 da su ka sace ana zargin maharan sun kashe wasu mutane sama da 20 a ƙauyukan.

A sakamakon hare-haren ƴan bindigan mutane da dama sun tsere zuwa cikin gusau daga ciki akwai mata masu ciki da ƙananan yara.

Daga ɓangaren gwamnati ta tabbatar da kai hari Garin Gebe kuma ya ce sojoji sun je sannan sun tarwatsa ƴan bindigan amma an yi wa wasu mutanen garin rauni.

Wasu na zargin an ƙone dukiyoyi da dama a sakamakon hare-haren da aka kai kauyukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: