Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane 7 a lokacin da ta ke gudanar da sintiri a karamar hukumar Birnin Kudu da kuma karamar hukumar Gwaram a Jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Lawan Shisu shi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin Labaran Najeriya NAN a yau Talata a  Dutse babban birnin jihar.
Shisu ya kara da cewa sun cafke mutane 3 ‘yan shekara 20 zuwa 28 a kauyen Babaldu da ke karamar hukumar Birnin kudu ta jihar ya ce sun kama su ne a lokacin da su ke gudanar da sintiri a yankin.
Ya kara da cewa sun samu tabar wiwi guda 85 da wasu kunshin kayan maye da yawan su ya kai 136 da jarkar sholiso 24 da kuma wuka guda daya.
Ya ce ragowar sauran mutane 4 an kama su ne a garin sabuwar gwaram da ke karamar hukumar ta gwaram a lokacin da ‘yan sandan su ka kai mamaya a yankin.
Shisu ya ce an kama mutane 4 ‘yan shekara 20 da 40 da sholiso.
Kuma ya ce da zarar sun kammala bincike akan su za su gurfanar da su a gaban kotu domin a yanke mu su hukunci

Leave a Reply

%d bloggers like this: