Shugaban kamfanin Kannywood Exclusive Isa Bawa Doro ya bayyana dalilin da ya sa su ka shirya wasan kwaikwayo mai suna Lu’u-Lu’u wanda ya nuna muhimmancin ƙananan sana’o’i tare da nuna muhimmancin dogaro da kai domin kawar da tunanin mutane daga zaman kashe wando a cikin al’umma.

Mashiryin shirin ya ce sun kalli yadda za su juyar da akalar fina-finan Hausa domin kallon wasu ɓangarori na al’umma kai tsaye tare da sanar da su irin alfanu da muhimmancin wasu abubuwa da mutane su ke da ƙarancin sani a cikin sa.

Wasan Hausa na Lu’u-Lu’u ya kalli ɓangaren sana’ar gwangwan wadda aka fi sani da jari bola tare da haska wa masu kallo irin alfanun da ke cikin ƙananan sana’o’i tare da kore zargi da ɓata sunan sana’ar kamar yadda mashiryin shirin Isah Bawa Doro ya shaida mana.

Lu’u-Lu’u shiri ne mai dogon zango wanda zai ci gaba a nitsa wa don zaƙulo wasu abubuwa da su ke faruwa a  cikin al’umma don ganin an fahimar da su muhimmancin ƙananan sana’o’i.

A yayin taron ƙaddamar da shirin, guda cikin  waɗanda su ka bayar da umarnin shirin Aminu Munnir K-Eza ya ce sun tsaya tare da kallon sana’ar har su ka ɗauki salon bayar da umarnin na daban yadda masu kallo za su fahimta.

Ibrahim Bala wanda ya rubuta labarin kuma ya tsara ya ce samar da aikin yi a tsakanin al’umma ne ya ja hankalin sa har ya rubuta labarin ta wannan fuska.

Lawal Ibrahim wanda aka fi sani da Bawan Mata ya ce mafi ƙarancin shekarun da za su ɗauka su na nuna shirin ba zai gaza shekaru uku ba.

Wasu daga cikin waɗanda su ka taka rawa a cikin shirin sun yi jawabi kamar haka.

Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya ja hankalin ƴan kasuwa da su shiga cikin sana’ar domin taimaka wa sana’o’in su da kuma ƴan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

A nasa ɓangaren guda cikin shugabannin masu ƙarfe a arewacin Najeriya Alhaji Sani Ya’u Jakara ya ce sun gamsu da yadda aka nuna wa duniya muhimmancin sana’ar su kuma za su ci gaba da bayar da gudunmawar su domin ganin an ci gaba da faɗakar da masu kallo muhimmancin dogaro da kai.

Shi ma Alhaji Shehu Usman mataimakin shugaban ƙungiyar masu sana’ar gwangwan ta arewacin Najeriya ya ce shirin ya ɗauki hankalin su duba ga irin ƙoƙarin da masu shirya shi su ka yi.

Taron ya samu halartar manyan ƴan masana’antar Kannywood da ƴan kasuwa na jihar Kano da wasu sannan jihohi ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

An ƙaddamar da shirin a ranar Litinin a Kano, kuma za a fara saka shi a dandlain Youtube daga ranar 1 ga watan Janairun 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: