Daga Amina Tahir Muhammad
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya aika da kudaden ribar man fitar na Naira biliyan 522.203 ga kwamitin kula da asusun ajiya na tarayya (FAAC) a cikin watanni 10.
An samar da kudaden ne daga watan Janairu zuwa Nuwamba,
A watan Mayu, kudaden da aka turawa FAAC ya ragu zuwa N38.608bn daga bisani ribar ta karu zuwa N47.162bn a watan Yuni kuma ya haura zuwa N67.280bn a watan Yuli kafin ya kai N80.030bn a watan Agusta.
An sake samun raguwar kudaden da ake turawa a kasashen waje tun daga watan Satumba inda kamfanin NNPC ya tura naira biliyan 67.533.
Rahoton da aka fitar na FAAC na NNPC a watan Nuwamba ya nuna cewa an samu karin kudaden da aka ware wa asusun tarayya na tallafin man fetur don tabbatar da cewa ya ci gaba da zama a farashin 162 da 165.
Akalla kamfanin NNPC ya kashe naira tiriliyan 1.159 kan tallafin a cikin watanni 10 na wannan shekara wanda ya fara daga watan Fabrairu zuwa Nuwamba.
Idan ba a biya tallafin ba, gwamnatin tarayya da Jihohi 36 da kuma kananan hukumomi 774 za su samu naira tiriliyan1.681 daga kudaden man fetur don rabawa, sai dai an bar su da naira biliyan 522 kawai.
Sai dai bayanai sun nuna cewa biyan tallafin naira tiriliyan 1.1 ne daga cikin kudaden da kamfanin NNPC ta yi, wanda ya rage kudin da ake nufi da FAAC.
Jumlar kudaden shigar cikin watanni goma sunkai naira tiriliyan 2.992 daga ciki ta cire naira tiriliyan 2.470, inda ta bar Naira biliyan 522 a matsayin kudin shiga ga FAAC.