Daga Amina Tahir Muhammad

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2021 kafin ranar 31 ga Disamba 2021.
Hakan ya biyo bayan mika kasafin da majalisar ta yi ga shugaban domin ya saka hannu.

Wata majiya daga majalisar ta ce an aike wa shugaban kasafin tun a ranar 24 ga watan da mu ke ciki, sai dai an kai washugaban a ranar 26 ga watan Disamba.

Majalisar ta musanta zargin da ake yi a kan cewar ba su aike wa shugaban kasafin fa.
Saka hannun shugaban shi zai bai wa majalisar dama mayar da kasafin doka don fara amfani da shi a shekarar 2022.