Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewar wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kashe mutane shida a jihar ciki har da basarake.

Ƴan bindiga sun afka garin Gada da ke ƙaramar hukumar Maru ta jihar.

An harbe mutane shida a ranar Laraba ciki har da Alhaji Umaru Bawan Allah wanda dagaci ce.

A yayin da aka kai harin, an sace mata da ƙananan yara waɗanda ba a tantance yawansu ba.

Sai dai jami’an tsaro ba su ce komai a dangane da lamarin ba.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren ƴan bindiga tsawon lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: