
Daga Amina Tahir Muhammad Risqua
Gobara ta kone kasuwanni biyu, Kasuwan Daji da Kasuwar Kara da ke Sokoto a ranar Larabar da ta gabata tare da lalata kayayyakin da darajarsu ta kai na miliyoyin naira.

Rahotanni sun cewa gobarar da ta tashi da misalin karfe 11:30 na safe har zuwa yamma kuma ta lalata sama da shaguna 150 a Kasuwan Daji.

Gobarar da ta tashi a kasuwar Kara da misalin karfe 7 na dare kuma ta fara ci har zuwa lokacin hada wannan rahoto tare da jami’an kashe gobara na tarayya da na jihar Sokoto su ka yi ƙoƙari don kashe ta.
Kawo yanzu dai ba a iya gano musabbabin tashin gobarar guda biyu ba.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu a Sokoto Bashir Jegawa wanda ya ziyarci kasuwar Daji, ya ce za a kafa kwamitin da zai tabbatar da barnar da aka yi domin samun tallafi.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Sokoto, Alhaji Chika Sarkin Gishiri, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asarar kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira.