Aƙalla mutane 12 ƴan bindiga su ka sace a ƙauyen Kerawa da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Mutanen da aka sace 10 daga cikin su mata ne sai kuma maza guda biyu.

A yayin da ƴan bindigan su ka kai harin an kashe mutum guda tare da jikkata wani guda ɗaya kuma tuni aka kai shi wani asibiti a Zaria.

Wani mai suna Jamil Kerawa ya ce babu wasu jami’an tsaro da su ke kula da su lamarin da ya sa ƴan bindiga ke kai hare-hare ba tare da tsagaita wa ba.

Mutanen yankin sun buƙaci gwamnatin jihar ta aike da jami’an tsaro yankin domin samin saukin hare-haren da su ke fuskanta daga yan bindiga.

Rundunar ƴan sandan jihar ba ta ce komai a dangane da harin da aka kai ba.

Mutane da dama ne ke hannun ƴan bindiga waɗanda aka sace a Kaduna, ciki har da wasu ƴan kasuwa da aka sace kwana nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: