Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da ƙara wa’adin hada layukan waya da lambar shidar ɗan’ƙasa.

A wata sanarwa da ministan sadarwa a Najeriya Dakta Isah Ali Pantami ya fitar, ya ce an ƙara wa’adin ne zuwa ranar 31 ga watan Maris na sabuwar shekarar da mu ke ciki.
Matakin hakan ya biyo bayan gano mafi yawan lambobi da ba a hada da katin lambar ɗan’ƙasa ba.

Hukumar yi wa yan ƙasa shaida NIMC ta ce ta yi wa sama da mutane miliyan 71 rijista daga lokacin da aka fara zuwa ranar 30 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Hukumar ta ce ta samar da wuraren daban-daban domin yi wa ƴan ƙasa rijista a cii da wajen Najeriya.
Hukumar ta amincewa wasu daga cikin euraren ibada, makarantu da asibitoci domin sauƙaka wa ƴan ƙasar wajen mallakar shaidar zama ɗan’ƙasa.
Hukumar sadarwa a ta ce ana iya hada lambobin waya guda huɗu da lambar ɗan’ƙasa guda ɗaya.
Sama da sau 5 hukumar na ƙara wa’adin da ta ke sanya wa domin bai wa ƴan ƙasar damar haɗa layukan wayar su da lambar ɗan’ƙasa.
An samar da tsarin ne domin taimaka wa tsaro a ƙasar wanda hakan ya zama babban ƙalubalen da ake fuskanta.