Rahotanni daga jihar Filato na tabbatar da cewar wasu da ake zargi yan bindiga ne sun yi awon gaba da wata amaryar da ta ke shirin angwancewa da mijinta.

An sace Farmat Paul a yankin Ngyong da ke ƙaramar hukumar Bokkos yayin da ake gab da ɗaura aure.
Shaidar gani da ido ya tabbatar da cewar ƴan bindigan sun zagaye gidan Parto ɗin da zai ɗaura auren sannan su ka ɗauke amaryar ita kadai.

Ƴan sanda sun ce ba su samu rahoto a kan faruwar lamarin ba.

Al’amarin ya faru a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10:45pm na dare.