Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayar da tabbacin kawo ƙarshen korona a cikin shekarar 2022.
Shugaban hukumar Tedros Adhanom ne ya bayyana haka ya ce zai yuwu a kawo ƙarshen cutar muddin ƙasashen duniya su ka hada kai aka yi aiki tare.
Ya ce akwai buƙatar ƙara dagewa a kan yadda duniya ke tafiyar da daƙile cutar a halin yanzu.
Hukumar ta buƙaci a yi wa kashi 70 na mutanen duniya riga-kafin cutar Korona domin sauƙaƙa dokokin da aka saka wa don hana yaɗuwarta.
Haka kuma akwai buƙatar ƙasashe su sake zage damtse domin ganin an kawo ƙarshen cutar a faɗin duniya.
Tuni wasu ƙasashen duniya su ka fara mayar da dokokin da za su taƙaita yaduwar cutar a cikin jama’a ciki har da ƙasar saudiyya.
Hukumar na kira ga al’umma da su ci gaba da bin matakan kariya domin hana yaɗuwar cutar tare da kawo ƙarshenta baki ɗaya.