Hukumar lura da jiragen ƙasa a Najeriya NRC ta bayyana cewar wa’adin da ta ɗauka don hawa jirgen kyauta ya cika.

Daraktan hukumar ne ya bayyana haka yau a Abuja ya ce za a ci gaba da siyar da tikitin jirgin daga yau da mislain ƙarfe 06:00 na yamma.
Gwamnatin tarayya ce ta bayar da garaɓasar hawa jiragen kyauta albarkacin kirsimeti da abuwar shekara.

Tun a ƙarshen watan Disambar shekarar d ata gabata ne gwamnatin ta sanar da hakan wanda aka shafe sama da kwanaki bakwai ana hawa jiragen kyauta.

Jihohin Legas, Oyo, Kwara, Kano, Kaduna da babban birnin tarayya Abuja na daga cikin jihohin da su ka mori garaɓasar.