Sabon nau’in cutar Korona mai ƙarfin gaske ya ɓulla a ƙasar Faransa.

Sabon nau’in mai suna COVID-19-IHU masana a ƙasar sun ce ya fi dukkan nau’in Korona da ke faɗin duniya.
Mutane 12 aka samu masu ɗauke da sabon nau’in cutar wanda tuni aka killace su.

Ƙasar Faransa ce tafarko da aka samu sabon nau’in cutar a halin yanzu.

Hukumar lafiya ta duniya WHO na yin nazari a kan sabon nau’in cutar kuma za ta yi cikakken bayani bayan kammala bincike a kai.
Wannan ne karo na huɗu da ake samun mabambantan nau’in cutar tun bayan samun ta a shekarar 2019.
Bayyanar cutar Korona ya haifar da koma baya a dukkanin ƙasashen duniya baki ɗaya.