Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce har yanzu bai tsayar da shawara a kan sake fitowa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023 ba.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da DW Hausa ranar Laraba.

Ya ce a halin da ake ake yanzu ba lokaci ne da zai yi gaggawar tsayar da shawarar hakan ba.

Kwankwaso wanda tsohon sanatan Kano ta tsakiya ne ya fito takarar neman shugabancin ƙasar a shekarar 2019 bayan komawarsa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.

“Mu na da mutane a Najeriya da sauran ƙasashen ƙetare ciki har da ƙasashen turai, amma hakan ba zai sa mu yi gaggawar tsayar da shawara ba a yanzu” Inji Kwankwaso.

Dangane da batun sake komawarsa jam’iyyar APC kuwa, kwankwaso ya ce sam ba shi da niyya koma wa jam’iyyar a halin yanzu.

Siyasa ta sake tsami tsakanin kwankwaso da gwamnan Kano Ganduje waɗanda ke yada magana a kan batun zaɓen 2019.

Leave a Reply

%d bloggers like this: