Daga Amina Tahir Muhammad

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare a Najeriya Zainab Ahmed ta ce babu wani shiri na korar ma’aikatan gwamnati kamar yadda wasu ke raɗe-raɗi a kai.
Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da aka yi da ita a shirin da aka yi da ita a gidan talabiji na NTA.

A yayin hirar ta musanta rade-radin da ake yi na cewa gwamnati na shirin korar ma’aikata ne domin ta tanadi kudade.

Ta ci gaba da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministar ta biya ma’aikatan gwamnati albashi.
Tun tuni ake raɗe-raɗin cewar gwamnatin na shirin rage ma’aikata yayin da ake ƙoƙarin haɗe wasu ma’aikatu a Najeriya.
Zainab Shamsuna Ahmed ta ce gwamnatin ƙasar na yin duk mai yuwuwa don ganin an samar da walwalar ma’aikatan ƙasar.