Gamayyar ƙungiyar masu siyar da kayan abinci da Naman shanu ta Najeriya sun bayyana cewa kudirin da kungiyar IPOB ta dauka na hana ‘yan kabilar ta cin naman shanu da yin taken Najeriya duk shirme ne.

Ƙungiyoyin sun bayyana hakan ne a jiya Laraba ta ce a shirye su ke da su dakatar da kai kayan abinci da sayar da shanu a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke mayarwa da ƙungiyar IPOB martani akan hana ‘yan kabilar ta cin naman shanu da kuma hana yin taken Najeriya ga kabilar.

Shugaban ƙugiyar Muhammad Tahir shi ne ya shaidawa kafar yada Labarai ta BBC cewa wannan umarni na kungiyar ta IPOB duk barazana ce.

Ya kara da cewa matukar kungiyar IPOB ba ta janye wannan kuduri na ta ba suma a shirye su ke su dakatar da kai kayan abinci yankin.
Ya ce Najeriya ta kasance kasar da al’umma su ke cike da hadin kai.

Ya kara da cewa matukar kungiyar IPOB ta hana kai abinci da nama yankin to al,umma da ke rayuwa a yankin za su shiga cikin wani hali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: